Connect with us

MAI KAMAR ZUWA, SHI AKAN AIKA Daga Abdul-Azeez Suleiman

News

MAI KAMAR ZUWA, SHI AKAN AIKA Daga Abdul-Azeez Suleiman

MAI KAMAR ZUWA, SHI AKAN AIKA
Daga Abdul-Azeez Suleiman
Lawal Adamu Usman wanda ake kira Mr LA, matashin dan siyasa, mai dattako da hangen nesa da karamci da tausayin alumma, ga far’a, ga kyauta shine wanda Jam’iyyar PDP a jihar Kaduna ta baiwa tikitin takarar Kujerar Sanata mai wakiltar shiyyar Kaduna ta tsakiya a zaben da zaa gudanar cikin watar Fabrairu mai zuwa, wato watan gobe.
Ga Kadan daga cikin kudurorin Lawal Adamu Usman, Mr LA don Kawo Cigaba Da Samar Da Kyakkyawan Wakilci Ga Jama’ar Kaduna Ta Tsakiya idan ya sami nasarar lashe zaben Kujerar Sanata don wakiltar kananan hukumomin Kajuru, Chikun, Kaduna ta Kudu, Kaduna ta Arewa, Igabi, Giwa da Birnin Gwari.
1. Mr LA zai samar da kyakkyawan wakilci ga Jama’ar mazabar Kaduna ta tsakiya ta hanyar tuntunba da neman shawarwarin su kafin ya dauki mataki akan alamurar da suka shafe su. Zai kasance yana maraba da kowa kamar yadda a yanzu kofar sa take bude, ba shamaki tsakanin sa da alumma maza da mata, manya da yara. Ba a yiwa kowa iso waurin Mr LA, ba a kuma nunawa kowa isa a gaban sa. Kowa nashi ne.
2. Mr LA zai bi duk hanyoyin da suka dace don ganin ya samar wa alumma mafita musamman ta fuskar inganta rayuwar matasa, da iyayen mu mata, da tsofaffi, da gajiyayyu, da masu karamin karfi da nakasassu. Zai samar was matasan yankin ayyukan yi, da bada fifiko wajen inganta rayuwar mata ta fuskar basu horo akan sana’o’in dogaro da kai.
a. Tuni ma har ya bude gidauniyar tallafi wanda ke daukan nauyin irin wadannan ayyuka da kudi aljihun sa. A halin da ake ciki dubbannin alumma maza da mata sun sami horaswa ta musamman a fannoni dabam dabam na rayuwa. Dubbanin jamaa maza da mata kuma sun amfana da tallafi iri dabam dabam kamar na ababen hawa wato motoci da babura, kayayyaki da nurorin zamani don sanaoi da kuma kudade don dogaro da kai.
b. Kananan yara da matasa maza da mata kuma sun amfana da tallafi don inganta ilimin su tun daga matakin firamare zuwa jamia, kai har ma da kasashen waje.
c. Sannan ana bayar da gudummawa na kudade da kayan aiki a makarantu na boko da na addini da kuma masallatai da majamiu. Bugu da kari a kokarin inganta wa alumma ayyukan addinin su, an dauki nauyin daruruwan jamaa marasa hali maza da mata don zuwa aikin hajji da umura ga musulmi da kuma kai ziyara Darassalamu ga mabiya addinin kiristanci.
d. Gidauniyar tallafin ta Mr LA ta kuma dauki nauyin kiwon lafiyan alummu da yawa maza da mata, sannan tana gudanar da ayyukan kyautata muhalli da suka hada da gine ginen gadoji, da magudanan ruwa da, rijiyoyin burtsatse, gyare gyare da kuma samar da sababbin tiransifomomin wutar lantarki, samar da cibiyoyin zuba share, da kafa injunan lantarki mai amfani da hasken rana a unguwanni dabam dabam.
e. Dangane da matsalar yawaitar mutuwar mata masu juna biyu a yayin haihuwa da jarirai kuwa, Mr LA nada kudurin kawo karshen wannan matsala ta yadda zai tabbatar da cewar an kara samar da cibiyoyin kula da lafiya matakin farko isassu a yankin Kaduna ta tsakiya, da kuma kawo kwararrun likitoci wadanda za su gudanar da ayyukan kula da lafiya.
3. Mr LA yana da kudurin inganta wasanni, kamar su kwallon kafa da sauransu. Ta wannan fuska zai yi kokarin ganin hazikan yan wasa sun sami daukaka ta hanyar sama masu gurabe a manyan kulob kulob a nan gida Najeriya da sauran kasashen duniya. Don kashin kansa zai yi kokarin samar wa yan wasa ingantattun filaye da kayan wasa da horaswa na zamani. Tuni ya fara tattaunawa da kulob kulob na unguwanni da dama don jin matsalolin su da kuma kokarin magance su. Kulob kulob da dama har sun amfana da gudummuwar sababbin rigunan wasa da kwallaye da kudade.
4. Hakazalika Mr LA nada kudurin yin dukkan mai yiwuwa don ganin an shawo kan matsalolin laifuffuka kamar shaye-shaye, karuwanci, fashi da makami da yin garkuwa da mutane da ke neman zama ruwan dare a Jihar. Zai yi hakan ta hanyar tsayin daka don ganin majalisa ta dauki kudurori na magance aukuwar laifuffuka ta hanyar inganta tsaro, tabbatar da adalci da bin kaida a ofisoshin yan sanda da kotuna, hana zaman kashe wando ta hanyar samar wa kowa abin dogaro da kai da kuma dakile talauci da lalaci da jahilci da zaluntar masu karamin karfi. Za a kuma bullo da hanyoyi masu inganci na ji koke-koken jamaa da ganawa akai-akai tsakanin alummu dabam dabam da mabiya addinai dabam dabam na jihar don samun daidaituwar fahimta.
(SULEIMAN SHINE DARAKTAN CIBIYAR LABARU NA KAMFEN DIN MR LA)

Continue Reading
You may also like...
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

More in News

To Top